✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kammala gasar kwallon Fibes a Kaduna

An kammala gasar wasan kwallon hannu na Fibes wanda Kaduna Fibes Club ta gudanar a filin wasan da ke dandalin Murtala Muhammad a Kaduna. Gasar…

An kammala gasar wasan kwallon hannu na Fibes wanda Kaduna Fibes Club ta gudanar a filin wasan da ke dandalin Murtala Muhammad a Kaduna.

Gasar ta samu halartar manyan bakin da suka hada da tsohon dan wasan kuma dattijon kasa Dan-Iyan Zazzau, Hakimin Kabala, Alhaji Yusuf Ladan, da shugaban kungiyar wasan kwallon Fibes na kasa Alhaji Sani Badamasi Abubakar da sauransu.
Wasan na fibes wanda aka fi yin sa a Arewacin kasar nan ana buga shi ne da hannu tsakanin ’yan wasa biyu ko hudua lokaci guda.
’Yan wasa da dama suka haye matakin wasan karshen inda Shehu Musa da Ibrahim danladi suka yi nasara akan Abubakar Isa (Zico) da Muhammad Usman (Diman).
A bangaren matsakaita kuwa, Ibrahim Muhammad da Mahmud Abubakar ne suka yi nasara akan danjuma Musa da Muhammad Adamu.
Wanda ya shirya wasan Muhammad danladi Isa ya ce ya dauki nauyin shirya wasan ne domin ganin an kara inganta kwarewa a tsakanin matasa.
Shi mi a nasa jawabin, wanda ya sanya kofuna guda biyu da aka yi gasa a kansu, kuma tsohon dan wasan, wanda shine Kwamishinan ma’aikatar kula da kananan Hukumomi na Jihar Kaduna Alhaji Shehu Ahmad (Giant) ya ce ba zai yi kasa a gwuiwa ba wajen ci gaba da tallafawa wasan Fibes don ganin ya bunkasa a kasa baki daya.