✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

 An kame mutum 6 kan zargin yi wa matar aure da wasu ‘yan mata 2 fyade a Kebbi

An kame wasu mutum shida kan zargin yin fyade ga wata matar aure tare da wasu ‘yan mata biyu, a kauyen Warra, cikin karamar hukumar…

An kame wasu mutum shida kan zargin yin fyade ga wata matar aure tare da wasu ‘yan mata biyu, a kauyen Warra, cikin karamar hukumar Ngaski ta Jihar Kebbi.

Kwamishinan ‘yan sandan Jihar Kebbi, CP Garba Danjuma, ne ya sanar da hakan yayin da yake yi wa manema labarai jawabi a yau Laraba, ya bayyana cewar, rundunar ‘yan sandan Jihar a wani sintiri ranar 22 ga watan Mayun shekarar nan, ta cafke wani mutum mai suna Usman Alhaji Lawal a kauyen Warrah, da kuma wasu mutum biyu su na kauyen Garin Baka na Karamar Hukumar Ngaski, kan laifin farma wata mata mai suna Safiya Audi, wadda matar aure ce, inda suka sassare ta da arduna, sa’annan suka kwace mata kudi Naira dubu 92,250 tare da yi mata fyade.

Kwamishinan, ya ce sun samu wasu shaidun da ke tabbatar da aikata wannan aika-aikar; kuma wadanda ake zargin sun amsa cewa sun aikata laifukan.