✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wata riƙaƙƙiyar mai satar wayoyin salula a Borno

Mun kama matar wadda aka fi sani da Bintu tare da abokin harkallarta.

Rundunar ’yan sandan Jihar Borno ta cafke wata mata da ta yi fice wajen kwace da satar wayoyin salula, wadda aka fi sani da Bintu, da wasu mutane 84 da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a jihar.

Laifukan da wadanda ake zargin suka aikata sun hada da hada da fyade, kisa, fashi da makami, sata, mallakar muggan makamai, da kuma mallakar tabar wiwi.

Da yake holen wadanda ake zargin a Maiduguri a ranar Alhamis, jami’in hulda da jama’a na ‘yan sandan, ASP Daso Nahum, ya ce sun aikata laifukan ne tsakanin 1 ga Oktoba zuwa 31 ga Disamba, 2023.

Ya bayyana cewa rundunar ta samu rahoton kararraki 49 kuma ta samu mutane 27 da ake tuhuma da laifi, inda ya ce ana kan bincike a kan kararraki 14 yayin da wasu 31 kuma aka gurfanar da su a gaban kotu.

ASP Nahum ya ce an kama Bintu da ke zaune a yankin Shehuri ta Kudu a Maiduguri, wadda a ranar 28 ga watan Disamban 2023 aka bayyana ana neman ta ruwa a jallo kan laifin satar wayoyin hannu.

“A binciken da ake yi, ta bayyana mana abokin harkallarta da ke zaune a unguwar Babban Layi a Maiduguri.

“Ababen zargin sukan yi dabarar ziyartar gidajen jama’a a matsayin masu aikin gida, inda suke tattare wayoyin salula na mazauna gidajen su kara gaba.

“A halin yanzu mun samu wayar salula daya kirar Techno LC6 a hannunsu yayin da ake ci gaba da bincike kan lamarin domin kama wadanda suke kaiwa wayoyin idan sun sata, saboda duk za a gurfanar da su a gaban kuliya,” in ji shi.

Nahum ya kara da cewa tun a ranar 31 ga Disamba, 2023, an kama hudu daga cikin wadanda ake zargi da laifin yayin da suka yi wani dandazo da makamai da kuma tabar wiwi.

Ya bayyana cewa an kwato kayan da ke hannunsu da suka hada da busasshen ganyen da ake zargin tabar wiwi ce, takobi daya, tukwane biyu da ake amfani da su wajen shakar wani abu mai sa maye da ake kira shisha, da wayoyin hannu guda biyar.

Ya ce za a ci gaba da gudanar da bincike kan wadanda ake zargin domin gurfanar da su a karkashin dokar hukunta manyan laifuka ta Jihar Borno.

Rundunar ta kuma kama wasu mutane takwas da ake zargin ‘yan kungiyar asiri ne ‘yan kasar Mali a lokutan bukukuwan Kirsimeti da na sabuwar shekara, inda ta kara da cewa an kama su ne a wani samame da aka kai a maboyar ‘yan ta’adda a Mairi, Fori, Tashan Bama, da Gwange.