Dubun wasu masu sana’ar hakar kabari ta cika bayan da aka zarge su da tone sababbin kaburbura, suka cire kawunan mutum biyar a wata makabarta a jihar Ondo.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sanda a jihar Ondo Tee Leo Ikoro, ya shaida wa Aminiya cewa wadanda ake zargin suna hannun rundunar, inda ake ci gaba da bincike a kan su.
Ya ce an kama wadanda ake zargin ne ranar Litinin, 25 ga watan Mayu, bayan sun hake wasu sabbin kaburbura da ba su wuce kwanaki biyu da binne gawarwakin cikin su ba.
“Wadanda ake zargin sun hadar da Oluwadare Idowu mai shekaru 67 da Adewale Abiodun mai kimanin shekaru 40, sai Akinola Sunday mai shekara 69 da Seun Olomofe da ke da shekaru 45.
“Lamarin ya faru ne a makabartar da ke karamar hukumar Akure ta Kudu, kana makabartar mallakin karamar hukumar ce, inda a nan wadanda ake zargin ke aikin hakar kabari.
“‘Yan uwan mamatan ne suka bankado lamarin bayan da suka koma makabartar da zummar yi wa kaburburan ‘yan uwansu daben siminti, amma sai suka iske an hake su an kuma cire kawunan gawarwakin, nan take kuma suka sanar da jami’an ‘yan sanda”, inji shi.
Ya kara da cewa a lokacin da aka kama wadanda ake zargin an same su da karin kan mutum hudu da su ma suka hako su daga makabartar.