’Yansanda sun kama wasu mutane da ake zargi da satar tumaki wadanda suka addabi mazauna kauyan Fanisau dake yankin karamar hukumar Dutse a jihar Jigawa.
Yunkurin kama mutanen ya biyo bayan yawaitar korafe-korafe ne da ofishin ’yan sanda na Fanisau ya samu a kan yawan sace masu tumaki, lamarin da ya sa jami’an tsaron daukar wasu matakai.
Hakan ya bai wa ’yan sandan damar gano wata duhuwa da mutanen da ake zargin barayin ne suke tara tumakin a wani daji kusa da kauyen Bakin Ruwa a kan hanyar zuwa Kano suna lodawa a mota suna kaiwa kasuwar bayan fage suna sayarwa.
- An cafke mutum 9 da ake zargin ’yan fashi ne a Jigawa
- Yadda farashin kaya ya yi tashin gwauron zabi a Jigawa
Kakakin rundunar ’yan sanda ta jihar Jigawa, SP Abdu jinjiri, ya tabbatar da faruwar lamarin yana cewa ’yan sandan sun kama wata mota kirar Sharon da ake kokarin loda tumakin a ciki.
Bugu da kari, daga cikin wadanda ake zargi da satar tumakin ’yan sanda sun kama mutane uku, yayin da biyu suka cika rigarsu da iska.
SP Jinjiri ya kuma ce tuni aka mika su sashen zurfafa bincike na rundunar domin fadada bincike a kan al’amarin, kuma da zarar an gama za a gurfanar da su a gaban kotu domin su fuskanci hukuncin da ya dace.