Rundunar ’Yan Sandan Jihar Ogun ta kama wani mutum bisa zargin shi da yi wa wata budurwa fyade a harabar coci.
Dubunsa ta cika ne bayan mika rahoton da mahaifiyar wadda abin ya faru a kanta ta yi ga ofishin ’yan sandan da ke yankin Lafenwa a Abeokuta.
- Alafin na Oyo, Oba Lamidi Adeyemi ya rasu
- Ranar littafi ta duniya: ‘Har a nade kasa ba za a daina karanta littafi ba’
Nan take DPO ya baza komar jami’an bincike domin kamo wanda ake zargin, wanda aka yi ram da shi ranar Alhamis, 21 ga Afrilu, 2022.
Da aka tsiye shi a wurin bincike, ya amsa laifinsa, cewa ya yi wa budurwar mai shekara 18 fyade a harabar coci.
Kakakin ’yan sandan Jihar Ogun, Abimbola Oyeyemi, ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan jihar, Lanre Bankole ya bada umarni a mika wanda ake zargin ga Sashen Binciken Manyan Laifuka na rundunar ta gudanar da cikakken bincike sannan a gurfanar da shi a gaban kotu.