An kama wani matashi mai shekara 24 bisa zargin sace wata budurwa ’yar shekara 13, da kuma yayi mata fyade har ta mutu a yankin Ejigbo na Jihar Legas.
Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Legas, Muyiwa Adejobi a cikin wata sanarwa ya ce abokanan matashin biyu da suka aikata ta’asar tare tuni sun cika bujensu da iska.
- An tsare magidanci kan zargin yi wa yara 10 fyade
- Matasa 4 sun yi wa ya da kanwa fyade a Bauchi
- Dattijo mai shekaru 60 ya yi wa ‘yar shekara 5 fyade a Bauchi
Sanarwar ta ce matasan uku sun yi wa budurwar jina-jina a fyaden da suka yi mata a wani daki, suka kama tafi suka kyale ta har ta mutu.
Rundunar ta ce a yayin da saurayin ke tsare a sashen binciken miyagun laifuka a reshenta da ke kan titin Panti, Yaba, an baza jami’ai domin taso keyar sauran masu ta’adar barnar.
Mista Adejobi ya ce matasan sun aikata mummunar ta’adar ne a ranar 30 ga watan Satumba, bayan mahifiyar yarinyar ta aike ta da misalin karfe 10.30 na dare.