✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama wanda ya yi kokarin yi wa ma’aikaciyar jinya fyade a Kano

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta kama matashin nan mai suna Bashir Yahaya da ke Unguwar Kofar Kabuga a Jihar Kano da ake zargi…

Rundunar ’yan sanda a Jihar Kano ta kama matashin nan mai suna Bashir Yahaya da ke Unguwar Kofar Kabuga a Jihar Kano da ake zargi da kokarin yi wa wata ma’aikaciyar jinya fyade.

An yi wa jami’ar jinyar wacce aka sakaya sunanta wannan aika-aika ne a daidai lokain da da take bakin aiki a wani asibiti da ke Tal’udu a Karamar Hukumar Gwale ta Jihar Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa bayan fyaden da ya yi kokarin yi wa jami’ar jinyar har ya kuma ji wani ciwo wanda ya yi kokarin kawo dauki ga ma’aikaciyar.

Kakakiun Rundunar ‘Yan sandan Jihar Kano DSP Abdullahi Haruna ya shaida

wa Aminiya cewa jami’an ’yan sanda ne suka kama wanda ake zargi a daidai lokacin da yake kokarin gudu bayan al’ummar unguwar sun yi kokarin halaka shi.

A cewar Kakakin Rundunar wanda ake zargin da kansa ya bayyana cewa ya yi kokarin yi wa matar fyade yayin da ta kuma ta bijirewa bukatarsa.

DSP Haruna Abdullahi ya bayyana cewa binciken ’yan sada na farko ya nuna cewa lokacin da wanda ake zargi yake kokarin gudanar da aika-aikarsa ne wani mai suna Zayyanu Abdulahmid ya ji motsinsu inda ya kawo mata dauki, “shi ma wanda ya kawo wa matar dauki mai suna Zayyanu Abdulhamid ya  samu rauni sakamakon yankar sa da wanda ake zargi da aikata laifin ya yi.”

Kakakin ’Yan sandan ya kara da cewa da zarar sun kammala bincik za a gurfanar da wanda ake zargi gaban kotu.