✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama tsoho mai shekara 60 da yin lalata da ‘yar shekara 10

Wani tsoho mai shekara 60 da ake zargi da yin lalata da yarinya ‘yar shekara 10 bayan ya bata Naira dari 6 ya shiga komar…

Wani tsoho mai shekara 60 da ake zargi da yin lalata da yarinya ‘yar shekara 10 bayan ya bata Naira dari 6 ya shiga komar ‘yan sanda.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Ogun DSP Abimbola Oyeyemi, ya shaidawa Aminiya cewa, iyayen yarinyar ne suka shigar da qara a ofishin rundunar da ke Arebge bayan da suka lura yarinyar ta sauya dabi’unta ko da suka tambaye ta sai ta fada masu tsohon ya bata Naira dari 6 yayi lalata da ita kana wanann shi ne karo na biyu.

Yanzu haka rundunar ‘yan sandan na bincike akan tsohon mai suna Taufik Shotayo da ke zaune a unguwar Obantoko a Abeokuta, za a kuma a gurfanar da shi a kotu domin fuskantar shari’a da zarar an kammala bincike kamar yadda DSP Abimbola Oyeyemi, ya sanar.