Wani mai shago da ake zargin yi wa wata yarinya kurma fyade da karfin tsiya a cikin shagonsa na sayar da kayan abinci ya shiga hannu.
Mutumin mai shekaru 34 da ake zargin ya amsa cewa ya yi lalata da kurmar akalla sau biyu a wurare daban-daban, a cewar ‘yan sanda.
Ammay ya ce da amincewar budurwar ya yi ta saduwa da ita ba da karfin tsiya ba kamar yadda ake zargi, don haka a cewarsa shi zina ya yi ba fayde ba.
Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Jigawa SP Audu jinjiri ya ce an kama mutumin ne bayan iyayen yarinyar sun kai koken zargin mutum da yi wa diyarsu kurma fyade, a kauyen Galanbi da ke Karamar Hukumar Gwaram a jihar.
- Ana yunkurin yanke hukuncin kisa kan masu fyade a jihar Neja
- An yi wa jaririya fyade bayan an sace ta
- Yadda Mai Siket ‘ya yi wa tsohuwa fyade’
SP Jinjiri ya ce an kai kurmar asibiti domin tantance ko ta dauki ciki ko wata cuta, yayin da shi wanda ake zargin, ake zurfafa binciken sa Sashen Binciken Manyan Laifuka na Rundunar domin tabbatar da gaskiya.
Da yake tabbatar da hakan, SP Jinjiri ya ce, dokar fayde tana aiki ne idan wanda aka yi wa ba ta kai shekara 15. Amma idan daga shekara 14 aka yi, ko da yandarta ne to ya zama fayde.
“Idan yarinya ta kai shekaru 15, in hakan ta faru da amincewarta ne ba da karfi ba to ya zama laifi ne na zina ba fyde ba, kuma da haka doka za ta yi wa wanda ya aikata hukunci”, inji shi.
Ya kara da cewar duk ko da yake mai shagon na ikirarin cewar da amincewarta ya yi lalatar da ita har sau biyu yin hakanma babban laifi ne. Saboda hakan za su gurfanar da shi a gaban shari’a.