Rundunar ’yan sanda ta bayyana nasarar da ta samu na kama wasu mutum biyu da ake zargin alakarsu da kungiyar asiri tare da kokon kan mutum a jihar Kaduna.
Kafofin watsa labarai da dama a kasar sun ruwaito Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan jihar, ASP Muhammad Jalige, ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Asabar.
- Gobara ta yi ajalin masu cutar Coronavirus 27 a Bagadaza
- Ramadan: Matasan Yobe sun tallafa wa ’yan gudun hijira
Sanarwar ta ce da misalin karfe 11.00 na daren Juma’ar da ta gabata ce aka sanar da jami’an tsaro cewar an ga wasu mutane a wata makarbartar musulmai da ke yankin Kudenden kuma ana tsammanin wani mugun nufi ya kai su.
“Bayan samun rahoton ne jami’anmu suka bazama kuma suka yi nasarar kama mutanen biyu da suka fito daga unguwar Zaki a yankin Kabala na Jihar.
“Yayin bincike, mun gano fatanya a tare da su da kuma kokon kan mutane,” a cewarsa.
ASP Jalige ya ce ana ci gaba da gudanar da bincike a kan mutanen kuma da zarar an kammala za’a gurfanar da su a gaban Kuliya.