Jami’an Rundunar Sojin Ruwa ta Najeriya a yankin Igbokada na Jihar Ondo sun kama mutum 24 da jiragen ruwa shida makare da man dizel da ake kyautata zaton na sata ne.
An cafke su ne dauke da kimanin lita 100,000 na man tsakanin gabar ruwan Jihohin Ondo da Legas.
- Gobara ta babbake rumfunan kasuwa 62 a Legas
- Buratai ya jinjina wa sojoji kan murkushe Boko Haram a Marte
Da yake gabatar da wadanda ake zargin a gaban ’yan jarida, Kwamandan Sansanin Rundunar a Jihar ta Ondo, Kaftin Sha’aibu Mohammed Ahmed ya ce sun kama jiragen ne dauke da man wanda ake kokarin yin safarar shi ta barauniyar hanya.
Ya ce daya daga cikin jiragen na dauke da ganga 150 na litar mai 250 na tataccen man na dizel.
Kazalika, wani jirgin ruwan kuma na katako sun kama shi dauke da tankoki 16 na litar man 4,500 kowannen su, yayin da sauran jiragen kuma suke dauke da gangunan da babu mai a ciki.
Rundunar ta sha alwashin ci gaba da yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta hanyar satar danyen man har sai ta ga bayansu.