✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mutum 1,200 bayan rikicin siyasa a Habasha

’Yan sanda a kasar Habasha sun bayar da sanarwar cewa sun kama mutum 1,200 da suke da alaka da rikicin siyasa mai zafi da ya…

’Yan sanda a kasar Habasha sun bayar da sanarwar cewa sun kama mutum 1,200 da suke da alaka da rikicin siyasa mai zafi da ya gudana a mako biyu da suka wuce.

Wannan shi ne karo na farko da aka yi irin wannan kamen, bayan da Firayi Minista Abiy Ahmed ya hau karagar mulki.

Akalla mutum 28 ne suka mutu a rikicin da ya faru a kusa da babban birnin kasar, Addis Ababa jim kadan bayan tsohon Shugaban kungiyar ’Yan tawayen kasar ta Oroma Liberation Front (OLF) ya dawo kasar.

Tuni dai kungiyoyin kare hakkin dan Adam irin su Amnesty International suka bukaci Firayi Ministan ya sako wadanda aka kama.

Haka kuma bayan wadanda aka kama masu alaka da rikicin, an sake kama wadansu kimanin 1,400 bayan an kai farmaki wajen da mutane suke taruwa, kamar wajen caca da shan shisha da sauransu, amma an saki wadansu daga cikinsu kamar yadda shugaban ’yan sandan kasar Majo Janar Degfie Bedi ya sanar da kafar Fana Broadcasting Corporate (FBC) ta kasar.

Tuni aka tura wadanda aka kama zuwa wani sansanin soja da ke Tolay, inda ake wani shiri na ‘canja musu tunani.”