Hukumar ‘yan sandan Najeriya ta kama mutum 12 da ake zarginsu da yin garkuwa da tagwayen Zamfara a ranar 21 ga Oktoba 2018 a kauyen Dauran Karamar Hukumar Zurmi da ke jihar Zamfara.
Kakakin hukumar ‘yan sandan Najeriya DCP Jimoh Moshood ne bayyana wadanda ake zargin a hedkwatar tsaro da ke Abuja, ya kuma ce an yi garkuwa da tagwayen ne Hassana Bala da Hussaina Bala lokacin da suke raba katin daurin aurensu.