Rundunar ƴan sandan jihar Kaduna ta kama mutane shida da take zargi da kashe Arɗon Zazzau da ƴaƴansa huɗu a ƙauyen Yan Durme dake ƙaramar hukumar Zaria.
Ranar Asabar 17 ga Yuni ne wasu mahara suka kashe Arɗo Alhaji Shuaibu Muhammad mai shekaru 80 tare da sace masa shanu fiye da 100.
Kakakin ƴan sandan jihar Kaduna, DSP Mohammed Jalige ne ya yi holin waɗanda ake zargi tare da wasu fiye da 500 da ake zargi da aikata wasu laifukan dabam.
Mahara sun kashe basaraken Fulani da ’ya’yansa 4 a Zariya
BIDIYO: An yi jana’izar mutumin da ’yan bindiga suka kashe tare da ’ya’yansa 4
Waɗanda ake zargin sun haɗa da Alhaji Adamu Haro (mai shekaru 58), Usman Adamu (mai shekaru 20), Abubakar Adamu (mai shekaru 18), Sani Alhaji Gambo (mai shekaru 35), Tukur Gambo (mai shekaru 25), da Haruna Adamu (mai shekaru 30).
DSP Jalige ya ce sauran mutane 503 da aka kama ana zarginsu ne da laifuffukan da suka haɗa da fyaɗe, fashi da makami, da satar kwangirin jirgin ƙasa.
Ya kuma ce rundunar na ci gaba da binciken waɗanda ta kama kafin gurfanar da su gaban kotu.