Hukumar Kare Hakkin Masu Sayen Kayayyaki ta Jihar Kano (CPC), ta ce ta kama mushen dabbobi a mayankar ’Yan Awaki da ke Unguwa Uku a karamar hukumar Tarauni da ke jihar.
Jami’in hulda da jama’a na hukumar, Musbahu Yakasai, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa ga manema labarai ranar Talata.
- Kotu ta soke zaben fid-da gwanin APC na Gwamnan Taraba
- Jami’iyya ta kori dan takararta kan yabon Hitler a Italiya
Ya ce, hukumar ta samu labarin dabbobin ne da misalin karfe 6:00 na safiya yayin da Babban mataimaki na musamman ga gwamnan jihar kan ingancin kayayyaki, Alhaji Salisu Muhammad, ya wakilci mai rikon shugabancin hukumar Baffa Babba Dan’agundi, a wajen kamen.
“Mun sami labari daga wasu mutane masu kishi cewa an kawo matattun dabbobi a mayankar da suka hada da raguna da awaki bayan an yanka su a wani waje.
“Nan take tawagarmu ta dauki mataki tare da kame dabbobin a kokarinmu na kare mutanen Kano daga amfani da kayayyakin na jabu da lalatattun kayayyaki”.
Ya ce hukumar ta gayyaci wani likitan dabbobi domin gwada dabbobin ko sun dace da cin namansu tare da tabbatar da ko da gaske ne yawancinsu sun mutu kafin a yanka su.
Haka kuma ya kara da cewa hukumar za ta yi maganin masu laifin yadda ya kamata.
Sanarwar ta kuma ruwaito cewa Babba Dan-Agundi ya bukaci mahauta da su daina aikata irin wannan mummunar ta’ada ko kuma su fuskanci fushin mahukunta.