’Yan sanda sun kama wasu motoci makare da buhunan tabar wiwi da kudinta ya kai Naira miliyan uku a cikin garin Kano.
An kama tabar wiwin ce a cikin wasu kananan motoci biyu a hanyarsu ta yin safarar miyagun kwayoyin zuwa wani wuri da ba a bayyana ba.
- Gwamnatin Taliban na son kasashen Musulmi su goya mata baya
- Karin kudin mai zai jefa karin ’yan Najeriya cikin talauci —Abdulsalami
Kakakin ’yan sandan Jihar Kano, DSP Abdullahi Haruna Kiyawa, ya ce, “’Yan sanda masu sintiri ne suka kama su da misalin karfe 3 na dare. Mutum na farko an kama shi ne a unguwar Naibawa na biyun kuma ya tsere, amma a hanya ya yi hatsari, aka kama shi a unguwar Birget.”
Ya ce dubun masu safarar kwayar ta cika ne a ranar 26 ga watan Disamba, 2021 a kan babbar hanyar Naibawa zuwa Zariya.
Daya daga cikin direbobin motocin da aka kama mai shekara 23, ya ce mutumin da suka dauko wa kayan ya tsere ne ya bar shi, bayan da ya lura cewa za a kama su, bayan sun yi hatsari.
“Na yi kokarin tserewa da motar a lokacin da ’yan sanda suka tsayar da mu, amma muka yi hatsari a hanya, mai tabar wiwin ya tsere ya bar ni ni kadai. Na yi da-na-sanin wannan abu kuma ba zan sake aikatawa ba.”
Daya direban kuma, mai shekara 28, ya ce bai san cewa tabar wiwi ba ce, sai da aka gama lodawa a motarsa.
“Na fito gida ne wani ya kira ni cewa mu je Naibawa Yanlemo akwai kayan da za mu dauka. Muna zuwa aka yi mana lodin buhunan, ban san cewa tabar wiwi ba ce ba sai da suka gama lodi.
“Na ce masa haka bai kamata ba, amma ya ce mu yi sauri mu bar wurin kafin wani abu ya faru. Hakan kuma aka yi,” inji shi.
Kiyawa ya ce Rundunar ’Yan Sanan Jihar Kano tana ci gaba da gudanar da bincike domin gabatar da wadanda ake zargin a gaban kotu.