Jami’an Hukumar Sibil Difens, sun kama wasu matasa biyu, kan zargin su da haƙar ma’adanai ba bisa ƙa’ida ba a yankin OkeIgbo a Ƙaramar Hukumar Ile- Oluji a Jihar Ondo.
Wata sanarwa da Kakakin Hukumar a Jihar, Mista Daniel Aidemenbor, ya sanya wa hannu, ta ce an kama matasan biyune bayan samun bayanan sirri.
- Yadda tsofaffi 3 ke fasa gidajen mutane suna sata
- Ambaliya ta lalata gidaje 2,517 da hektar gonaki 1,000 a Gombe
A wani labarin, Aidemenbor ya ce jami’an hukumar sun kama wani da ake zargin da satar manyan wayoyi na Kamfanin Recline Cable.
Wanda ake zargin mai suna Segun Alao, mai shekara 40 wanda ma’aikacin kamfanin ne, sannan ana zarginsa da satar janareta da silin da da kuɗinsu ya kai Naira miliyan 3.5
An kama shi ne a titin Araromi da ke garin Akure, kuma da zarar an kammala bincike za a gurfanar da su a gaban kotu.