Jami’an tsaron ƙasar Saudiyya sun kama wasu mata biyu da ake zargin cewa mata da kuma mahaifiyar jagoran ’yan bindiga da gwamnatin Najeriya ke nema ruwa a jallo, Ado Aliero, bayan sun je aikin Hajji.
An kama matar Aliero da mahaifiyar tasa ne a birnin Madina bayan sun je yin ziyara gabanin fara aikin Hajji.
Ado Aliero shugaban ’yan bindiga ne da ya yi ƙaurin da yin garkuwa da mutane masu yawa a lokaci guda, musamman a Jihar Zamfara da maƙwabtanta.
Kafar yada labarai ta ABN News ta bayyana cewa matan biyu sun canza sunayensu domin kada a gane su.
- An cimma matsaya kan dakatar da haska fina-finai 22 a Kano
- Yadda Boko Haram ta kashe manoma 90 a Borno cikin wata 5
Kamen nasu ya zama wani sabon a yadda gwamnatin Najeriya ke aiki tare da ƙasashen duniya wajen magance matsalar ta’addanci.
An bayyana cewa Gwamnatin Najeriya tana aiki tare da Saudiyya a yayin da ake zurfafa bincike kan matan da ake zargi.
Ba a bayyana sunayen matan a hukumance ba, amma majiyoyin tsaro sun bayyana cewa akwai yiwuwar a tatsi muhimman bayanai daga gare su.