✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama matar da ta yi yukurin sace jariri

A ranar Asabar da ta gabata ce aka kama wata mata da ake zargi da yukurin sace wani jariri dan wata tara da haihuwa a…

A ranar Asabar da ta gabata ce aka kama wata mata da ake zargi da yukurin sace wani jariri dan wata tara da haihuwa a asibitin Yusuf Dantsoho dake Tudun Wada a Kaduna.

Lamarin ya faru ne da misalin karfe 10 na safiyar ranar a lokacin da yaron ke kwance a gadon asibiti. Aminiya ta samu labarin cewa mahaifiyar yaron ne ta kama matar, bayan ta dauki yaron daga kan gadonsa tana shirin tserewa.

Wakilinmu ya ziyarci asibitin domin ganawa da mahaifiyar yaron da aka nemi sacewa, amma sai ya iske cewa tuni an sallameta. To amma sai dai daya daga cikin ma’aikatan asibitin mai suna Muhammed wanda ya tabbatar wa Aminiya da faruwar lamarin ya bayyana yadda abin ya faru.

Ya ce “ina zaune da masu gadin asibitin a bakin kofar shigowa cikin asibitin sai na hango daya daga cikin masu tsaron asibitin rike da wata mata a hannunsa. Sannan kuma ga mata nan da yawa suna biye da shi suna bugun matar.

“Da ya zo sai ya bayyana mana cewa an kamata ne ta sace jariri mara lafiya dake kwance akan gado, saboda yawan mutanen da suka taru suna kokarin halaka matar, sai muka sakata cikin dakin masu gadi kafin muka sanar da ‘yan sanda abin da ke faruwa,” inji shi.

Muhammed ya kuma bayyana cewa koda yake wanda ake zargin ta karyata zancen, domin a cewarta wai yaron na kokarin fadowa ne daga kan gadon da yake kwance, shi ne ta dauke shi.

“Mun tambayeta ko ta zo jinyar wani ne a asibitin ko kuwa ziyara ta kawo, sai ta ce mana wai ta shigo asibitin ne kawai, amma ba ta jinyar kowa. Koma dai menene mun rigaya mun mika ta ga ‘yan sanda saboda tsoron kada mutane su kashe ta a cikin asibiti,” a cewarsa.

Ita ma shugabar ma’aikatan jinya ta asibitin, Jamila Garba ta ce ta samu labarin abin da ya faru, kasancewar ba ta cikin asibitin a ranar da abin ya faru. Dan haka sai ta yi kira ga mata musamman masu jinya da masu zuwa ziyara da su rika kiyaye lokacin ziyara na karfe 4 zuwa 6 na yamma, domin mutane su daina shiga dakunan marasa lafiya ba tare da ka’ida ba.