✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama matar da ta boye dauri 100 na hodar iblis a al’aurarta

Ta cusa kunshin hodar a al’aurarta bayan ta gaza hadiye ta.

An cafke wata mata da ta boye miyagun kwayoyi a al’aurarta a yayin da ta yi fasakwaurinsu daga Brazil zuwa Najeriya.

An cafke matar ce da kulli 100 na hodar iblis da ta boye a cikin al’aurarta da kuma kakarta ta hannu a daren Juma’a bayan saukarta filin jirgin saman Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.

Matar mai suna Anita Ugochinyere Ogbonna ta shiga hannun Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi (NDLEA) bayan zuwanta Najeriya daga birnin Sao Paolo na Brazil inda ta ratso ta birnin Doha na kasar Qatar.

Kakakin NDLEA, Femi Babafemi, ya ce matar mai ’ya’ya uku yayin bincike sun gano kunshin hodar iblis 12 da boye a cikin al’aurarta da kuma kunshi 88 da ke cikin jakarta ta hannu.

Ya ce ta amsa laifinta inda ta ce ta shiga wannan harka ne domin tara kudin binne mahaifinta wanda za a yi jana’izarsa a ranar 22 ga watan Yuli a Jihar Imo.

“Ta ce wani mutum mai suna Emeka da ke zaune a Brazil ne ya bata kunshin hodar ta kawo Najeriya a kan zai biya ta ladan Dala dubu uku.

“Ta ce ta cusa kunshin hodar ce a al’aurarta bayan ta gaza hadiye ta.

“Matar ta ce tana sayar da abincin gargajiya ne a Brazil, inda a bar ’ya’yanta uku a hannu wata mata ’yar kasar Kenya kafin ta yi wannan balaguro,” a cewar Babafemi.