Rundunar ’Yan sandan Jihar Bayelsa ta kama wadansu matasa biyar da ake zargi da yunkurin kona gidan tsohon Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan da ke Yenagoa babban birnin jihar. Mutanen kamar yadda Aminiya ta samu sunayensu su ne Asupha Emeka da Ebipre Ebebi da Samuel Joe da Okilo Matthew da Timiere Matthew.
An kama mutanen ne a wani otel mai suna Swali lokacin da suke kulle-kulle kan yadda za su kai hari a gidan tsohon Shugaban kasar.
An yi zargin sun kulla harin ne ganin cewa gobe Asabar ce ake zaben cike-gurbi a karamar Hukumar Ijaw ta Kudu don dagula zaben. Kuma an yi zargin ’yan ta’addan magoya bayan wani fitaccen dan siyasa ne a jihar.
Da Aminiya ta tuntubi Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bayelsa, Asinim Butswat game da batun ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Wasu mazauna garin Yenagoa da aka ji ta bakinsu game da wannan yunkuri, kuma suka bukaci a sakaye sunansu sun ce yunkuri ne da aka kitsa domin a bata sunan jamiyyar adawa a jihar a ce ita ce da alhakin haka “Domin ai jagoran kai harin dan jam’iyyar tsohon Shugaban kasar ne,” inji daya daga cikinsu.
An kama masu yunkurin kona gidan Jonathan
Rundunar ’Yan sandan Jihar Bayelsa ta kama wadansu matasa biyar da ake zargi da yunkurin kona gidan tsohon Shugaban kasa Goodluck Ebele Jonathan da ke…