✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu kwacen waya a Sallar Tahajjud a Kano

An cafke mutum 16 da ke yi wa masu Sallar Tahajjud kwacen wayoyi.

Wasu masu kwacen waya a wurin Sallar Tahajjud a Kano su 16 sun shiga hannu.

Rundunar ’yan sandan Jihar Kano ta cafke matasan da suka kware wajen kwacen wayoyin bayan sun fito a cikin dare da niyyar yi ta’asar.

’Yan sandan daga rundunar Kan Ka ce Kwabo sun kai samamen tare da kame matasan ne bayan yawaitar korafe-korafen mutane kan kamarin.

“Matasan sukan fita ne a cikin dare da misalin karfe 2 zuwa 3 suna kwacen wayoyin mutane.

“Bayan samun korafe-Korafe, Kwamishinan ’Yan Sanda Sama’ila Shu’aibu Dikko ya ba da umarnin baza koma kuma aka yi nasarar kamo mutum 16 daga cikinsu,” inji kakakin ’yan sandan jihar, Abdullahi Haruna Kiyawa.

Ya ce an samu masu kwacen wayoyin ne dauke da muggan makaman da suke amfani da su wurin yi wa mutanen da suka fito Sallar Tahajjud barazana suna kwace musu wayoyi.

Ya kara da cewa, a daren ranar Litinin ne Rundunar ta cafke matasan, wadanda wasu daga cikinsu suka shada wa Rundunar cewa fadan daba ne ya fito da su, sauran kwacen waya suka fito yi.

Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kano, Sama’ila Shu’aibu Dikko, ya ja hankalin jama’ar jihar, da su kasance masu bayar da bayanai ga jami’an tsaro, don kawo karshen masu aikata miyagun laifuka a fadin jihar.