✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama masu garkuwa da mutane a Borno

A ranar Larabar makon jiya ce Rundunar ’Yan sandan Jihar Borno ta ce ta samu nasarar kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane lokacin…

A ranar Larabar makon jiya ce Rundunar ’Yan sandan Jihar Borno ta ce ta samu nasarar kama wadanda ake zargi da yin garkuwa da mutane lokacin da suka je karbar kudin fansa Naira miliyan 21 a kauyen Tuga da ke Karamar Hukumar Damboa a jihr.

Kwamishinan ’Yan sandan Jihar, Mista Damian Chukwu ya bayyana wa manema labarai haka a ofishinsa lokacin da yake gabatar da wadanda ake zargin su hudu.

Daya daga cikinwadanda ake zargi da  garkuwa da mutanen mai suna Musa Haruna mai shekara 74, ya musanta zargin inda ya ce “A’a ba haka ba ne, wadansu mutune a bara sun sace mini shanu 47 da  tumakanmu 83, shi ne sai muka shirya da wadannan mutanen da kuma wadansu cewa su je su kamo wadanda suka sace shanun. To mun san yanzu babu shanun, shi ya sa na ce to a rike shi har sai ’yan uwansa sun kawo mana Naira miliyan 21.”

“Idan suka kawo mana sai mu sake shi, wannan a kan gaskiyarmu muke, domin muna neman hakkinmu ne kuma muna da tabbacin su ne suka kora mana shanun, to kuma ba wata hukumar da za mu iya kai kara a share mana hawaye, shi ya sa muka yanke shawarar kamo shi mu boye  don ’yan uwansa su biya mu. Wannan ba za a ce garkuwa ba ne, tunda wajen neman hakkinmu ne, don su ne suka kora mana dabbobinmu,”  inji shi.

Game da ko da gaske ne an kama su da makamai, sai Malam Musa Haruna, ya ce “To ai wadannan makaman da kake gani dole ne mu rike su saboda kariya ne a gare mu, a matsayimu na Fulani makiyaya kuma mazauna cikin daji, domin mutum ba zai zauna haka nan ba makami ba. Kuma gaskiya ce ’yan sanda sun zo sun kama mu a ranar da muka yi da ’yan uwan wancan da muka kama za su kawo mana kudi Naira miliyan 21, domin sun zo ne tare da ’yan sandan, amma kuma kudin bai cika ba, to amma dai gaskiya na yi nadamar aikata hakan, saboda ban bi hanyoyin da suka dace ba wajen neman hakkin nawa.”