Rundunar ’yan sandan Najeriya ta sanar da kama wasu da take zargin masu garkuwa da mutane ne su tara a Jihar Ekiti.
Mutanen da aka kama a garin Ago Adulojh da ke Ado Ekiti, sun shiga hannu ne a kokarin rundunar na kakkabe yan ta’adda daga cikinta.
- Gwamnati za ta fara daure Iyayen mabarata a Edo
- An dakatar da hakimai 4 saboda saba wa dokar Hawan Sallah a Zazzau
Kakakin rundunar, ASP Sunday Abutu ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin.
A cewarsa, sun sami wannan masara ce a sakamakon wasu bayanan sirri da suka samu kam yadda wadanda ake zargin suka yi wa dajin Agon dirar mikiya.
An kama su ne a dajin wanda tun a baya ke da tarihin zama mafakar masu aikata laifuka.
Kwamishinan ’yan sandan jihar CP Morenkeji Adesina ya tabbatar wa al’ummar jihar cewa ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen kama bata gari da daukar mataki kansu.