Rundunar ’Yan sandan Jihar Kebbi ta kama mutum 81 da take zargi da yin garkuwa da mutane da kum fashi da makami da aikata wasu miyagun ayyuka.
Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Alhaji Garba Muhammad Danjuma ne ya bayyana haka lokacin da yake gabatar da wadanda ake tuhuma ga manema labarai a hedkwatar ’yan sandan jihar da ke Birnin Kebbi.
Kwamishina Garba Muhammad Danjuma ya ce su wadannan mutane ana tuhumarsu ne da garkuwa da mutane da fashi da makami da kashe ’yan acaba da kuma aikata ta’addanci ga al’ummar Jihar Kebbi.
Kwamishinan ya ce yawancin wadanda ake tuhuma ’yan asalin Jihar Kebbi ne kuma sun fito ne daga garuruwan Birnin Kebbi da Yawuri da Koko da Jega da Mahuta da Kangiwa da Warra da Zuru Argungu da Kanya da Danko-Wasagu da Suru da Dolekaina, sai kuma wadansu ’yan asalin Jihar Neja da suka fito daga Kwantagora da Salka da Nasko da kuma Borgu.
Kwamishinan ya ce daga cikin wadanda ake tuhumar akwai guda biyu da ake tuhuma da kashe matar yayansu saboda tana yi masu nasiha su bar yin sata, su ne Jamilu Musa da kuma Alhaji Alu wanda yake bebe ne.
Kwamishinan ya ce mutanen sun bari dare ya yi ne suka samu igiya suka sanya wa matar a wuya suka zarge igiyar da karfi sai da ta mutu, bayan haka suka dauki ’yarta ’yar shekara 3 suka sanya ta cikin akwati har sai da ita ma ta mutu.
Kwamishinan ya ce yanzu haka za a tura su kotu domin yanke musu hukuncin da ya dace da su.
Kwamishinan ya yi kira ga al’ummar Jihar Kebbi su rika hada kai da jami’an tsaro domin tona asirin duk wanda ba su yarda da shi ba, domin harkar tsaro ba ta dan sanda kawai ba ce musamman yanzu da ake tarwatsa ’yan ta’adda a Zamfara, inda ya ce idan ba a yi hankali ba duk wadanda suka samu tserewa daga Zamfara za su iya gangarowa jihohin Kebbi da Neja, saboda haka dole ne kowa ya sa ido domin bai wa jami’an tsaro hadin kai.Kwamishinan ya nanata kudirinsa na kare al’umma da dukiyoyinsu a duk fadin Jihar Kebbi.