Jami’an tsaro a Jihar Oyo sun yi nasarar kama mutane 5 daga cikin kimanin 20 da ake zargi da yunkurin kwace harkokin watsa shirye shirye a gidan Rediyon Najeriya Amuludun 99.1 (FM) domin yada da’awar kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa.
Da yake tabbatar da lamarin a wajen taro da ’yan jarida a Ibadan, Kwamishinan ‘yan sanda na Jihar Oyo, CP Adebowale Williams ya ce da misalin karfe 6 na safiyar yau Lahadi ne suka yi ta samun kiran wayar wasu mutane a game da yunkurin kwace gidan Rediyon.
- Harkar fim ta kai ni inda ban zata ba — Adaman Kamaye
- Sabon salon zuba lefe a firinji ya kunno kai a Kano
Ya ce Rundunar ‘Operation Burst’ da ke aikin sintiri a lokacin ta hanzarta kai dauki kuma ta yi nasarar dakile wannan yunkuri tare da cafke mutum biyar daga cikin ababen zargin.
Kwamishinan ya bayar da sunayen mutane biyar da aka kama da suka hada da Noah Atoyebi mai shekara 30 da Gbenga Aseleke dan shekara 25 da Abdulganiyu Mustapha Kolawole mai shekara 35 da Fajola Elija mai shekara 45 da wata mata mai suna Kehinde Bashiru da ba a fadi yawan shekarunta ba.
Da yake yi wa ’yan jarida karin haske Babban Manajan gidan Rediyon, Mista Stephen Agbaje ya ce al’amuran gidan Rediyon sun dawo kamar yadda aka saba bayan jami’an tsaro sun dakile yunkurin wadannan mutane.
Binciken da Aminiya ta gudanar ya nuna cewa wadannan mutane da yawansu ba zai kasa da 20 ba sun yi wa gidan Rediyon dirar mikiya ne da sanyin safiyar yau Lahadi a inda suka zagaye harabar gidan Rediyon suka shiga cikin dakin watsa shirye shirye da suka shafe kimanin awa daya suna gudanar da shirye shirye da kansu kafin isowar jami’an tsaron hadin guiwa na ’yan sanda da sojoji da suka dakile mummunan nufin na su na kafa kasar Yarbawa ta Oduduwa.
Binciken ya tabbatar da cewa a lokacin da wadannan mutane suka fara gudanar da shirye shirye da kansu sun yi ta ambaton cewa kasar Oduduwa zama daram sannan kuma kasar Yarbawa a yanzu ba ta karkashin Gwamnatin Tarayyr Najeriya hadi da cewa nan gaba kadan Majalisar Dinkin Duniya za ta ayyana Oduduwa Nation a matsayin kasa, “Oduduwa Nation has come to stay” da “Yoruba no more under Federal Republic of Nigeria” da kuma “United Nations will soon declare Oduwa Nation.”
Wannan lamari dai na zuwa ne a daidai lokacin da ya rage kwana daya kacal a rantsar da sabon zababben Shugaban Kasar Najeriya, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu wanda asalinsa ya fito ne daga wannan sashe na Kudu maso Yamma mai kunshe da kabilar Yarbawa zalla.