✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama masu casun tsiraici a Bauchi

Matsa 19 da shekarunsu ba su fi 22 ba masu badalar da suka hana jama’a sakat

’Yan sanda a Jihar Bauchi sun kama gungun wasu matasa 19 da suka shirya casun tsiraici a Jihar.

Dubun bata-garin masu shekaru 19 zuwa 22 ta cika ne bayan sun shirya sharholiyar tasu a Karamar Hukumar Dass ta Jihar Bauchi.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Ahmed Mohammed Wakil ya ce bayan samun bayan sirri ne Rundunar ta fara aiki ba dare, ba rana domin kawo karshen gungun bata-garin.

Ya kara da cewa gungun matasan sun addabi jama’ar Dass da kwacen waya da sauran nau’uka na fitsara ciki har da gudanar da casun tsiraici.

DSP Lawal ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Lawan Tanko Jimeta, ne da kansa ya tura tawagar Rundunar Kar-ta-kwana (RRS) domin cafko su.

Ya ce bayan kammala binciken matasan da shekarunsu bai haura 22 ba za a gurfanar da su a gaban kotu.