✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mai shekaru 52 da dala miliyan 4.7 na jabu a Abuja

An yi yunkurin sace kusan naira biliyan 2.7 na tattalin arzikin Najeriya.

Jami’an Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun Kwayoyi ta NDLEA sun kama wani mutum mai shekara 52 da makudan daloli na jabu a Abuja, babban birnin Najeriya.

Sanarwar da hukumar ta fitar ta ce an yi yunkurin sace kusan naira biliyan 2.7 na tattalin arzikin Najeriya ta hanyar tura kudaden na jabu a kasuwa da suka kai sama da dala miliyan 4.7.

Hukumar ta ce jami’anta sun kama kudaden a yankin Abaji da aka dauko daga Legas zuwa Abuja.

Da yake zantawa da manema labarai a ranar Lahadi, Femi Babafemi, ya ce an kama wanda ake zargi da fataucin kudin mai suna Abdulmumini Maikasuwa.

Hukumar ta ce shugabanta Birgediya Janar Buba Marwa ya bayar da umarnin a mika kudaden da wanda ake zargi ga hannun Hukumar Yaki da Masu Yi wa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati ta EFCC domin ci gaba da bincike.