✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama mai garkuwa da mutane da kubutar da mutum 8 a Kaduna

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kubutar da yaro dan shekara 13 da wasu mutum 7 da aka yi garkuwa da su a Rigasa, Maguzawa…

Rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna ta kubutar da yaro dan shekara 13 da wasu mutum 7 da aka yi garkuwa da su a Rigasa, Maguzawa da dajin Gurguzu duk a cikin jihar.

An kama mai garkuwan da mutanen mai suna Mustapha Ibrahim wanda yake zaune a hanyar Daura cikin garin Kaduna lokacin da yake hanyarsa na mika wadanda aka yi garkuwan da su ga wani Abubakar Aminu shi da tawagarsa da ke kauyen Maraban Rido a Karamar Hukumar Chikun jihar Kaduna.

A cewar jami’in Hulda da jama’a na Hukuamar ‘ya sandan jihar DSP Yakubu Sabo, ya ce wanda ake zargin  shi ne ya bayyana sirrin yadda aka kubutar da mutum biyu masu suna: Ismaila Hussaini da Hussaini Umar daga cikin wadanda aka yi garkuwa da su a maboyar ‘yan bindigar. Wadannan suna zaune ne a yankin Ado-Gwaram unguwar Rigasa Kaduna.