✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama mai gadi kan yi wa ’yar makwabcinsa fyade a Abuja

Yanzu haka yarinyar tana asibiti ana duba lafiyarta

Rundunar ’Yan Sanda ta yankin Babban Birnin Tarayya Abuja ta kama wani mai gadi mai shekara 48 kan zarginsa da yi wa ’yar makwabcinsa mai shekara 10 fyade.

Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar a yankin, S.P Josephine Adeh, a wata sanarwa da ta aika wa Aminiya a yammacin Lahadi, ta ce an kama wanda ake zargin ne daga babban ofinsu na Apo a Abuja.

Ta ce an kama mai gadin ne bayan mahaifiyar yarinyar, wadda a ka sakaya sunanta, ta kai kararsa.

Sanarwar ta ce mahaifiyar yarinyar da ke zama a kusa da rukunin gidaje na Prince and Princess da ke yankin na Apo Abuja, ta yi korafin cewa mutumin ya lalata mata yarinyar.

“Bayan gudanar da bincike a kansa, wanda ake zargin ya amince a rubuce cewa ya aikata lalata da yarinyar a lokuta da dama,” in ji Josephine Adeh.

Ta ce rundunar za ta gurfanar da wanda ake tuhumar a gaban kotu da zaran an kammala bincike.

Ta kuma ce yanzu haka ana ci gaba da tantance lafiyar yarinyar a asibiti.

Jami’ar ta rawaito Kwamishinan ’Yan Sanda na Abuja, C.P Sadiq Idris Abubakar, na horon iyaye kan su kula tare da sa ido kan zamantakewar ’ya’yansu don gudu mu’amala da bata-gari.