A ranar Asabar da ta gabata ce ’yan sanda suka kama Ted Terry mahaifin tsohon Kyaftin din kulob din Chelsea John Terry saboda cin mutuncin da ya yi wa farkarsa mai shekara 42 mai suna Ebelyn Minkey.
Ted Terry mai shekara 65 ya bi farkar tasa Ebelyn har gida ne da tsakar dare ranar Asabar da ta wuce inda ya ci mutuncinta ta hanyar zagi da duka. Sai dai rahoton bai bayyana dalilin da ya sa Ted Terry ya nemi farkar tasa da fada ba.
Rahoton da jaridar Sun ta Ingila ta kalato ta ce ana zargin Ted Terry ya yi tatil da giya ce lokacin da ya bi farkar tasa har gida don cin mmutunci.
Da Ebelyn ta ga abin ba sauki sai ta zura a guje ta rika neman taimako daga makwabta don su kira ’yan sanda. Kuma cikin kankanen lokaci sai motar ’yan sanda dauke da jami’ai 12 suka kai dauki inda suka kama Ted Terry wanda ko riga babu a jikinsa a lokacin faruwar lamarin al’amarin da ya sa ake masa kallon ba ya cikin hayyacinsa.
Dansa John Terry yanzu haka shi ne Mataimakin koci a kulob din Aston Billa na Ingila.