Rundunar ’Yan Sandan Kasar Senegal ta kama wasu ma’aikatan lafiya biyu bayan mutuwar sabbin jarirai 11 sanadiyyar gobara a makon da ya gabata yayin da suke bakin aiki.
Wani gidan rediyo mai zaman kansa a kasar na RFM ne ya rawaito tsare ma’aikatan a ranar Lahadi.
A ranar Laraba ne dai wata ma’aikaciyar jinya da mataimakiyarta da ke cikin wadanda aka kama ke bakin aiki a asibitin Abdoul Aziz Sh Dabakh da ke birnin Tivaoune da ke kusa da babban birnin kasar wato Dakar lokacin da lamarin ya faru.
An dai kama su ne bisa zargin yin shakulatin bangaro da jariran yayin da suke bakin aiki, hadi da sanya rayuwarsu cikin hatsari, kamar dai yadda gidan rediyon RFM din ya sanar.
Kamen dai na zuwa ne kwanaki kadan bayan shugaban kasar Macky Sall yayi alkawarin binciken sanadiyar tashin gobarar a asibitin.
Ya kuna kira da a tantance dukkanin kayan aikin sashin kula da jariran da ke asibitocin fadin kasar.
A makon da ya gabata ne dai an dai kori ministan lafiya Abdoulaye Diouf Sarr na kasar, in da aka maye gurbinsa da babban jami’in ma’aikatar Marie Khrmesse Ngom Ndiaye, kamar dai yadda gwamnatin ta bayyana.