’Yan sanda sun kama wasu limaman coci biyu bisa zargin yi wa wata mai yi wa kasa hidima fyade a karamar hukumar Obio/Akpor ta Jihar Ribas.
Limaman cocin da aka kama, Austin Emmanuel da Peter Davis a yanzu haka suna tsare a sashen binciken manyan laifuka na Rundunar ’yan sanda a birnin Fatakwal.
- Bango mai shekara 100 ya kashe matar aure a Katsina
- ‘Yadda ’yan bindiga suka kashe dana suka sace iyalina 17’
Bincike ya nuna cewa, Emmanuel ya gayyaci matashiyar mai shekara 27 gidansa domin ta taya shi bikin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, sai daga baya Davis ya shigo gidan.
Matashiyar ta ce, limaman sun yaudare ta ne da cewar za su yi mata addu’a inda suka watsa mata wani ruwa a fuska da ya sa hankalinta ya gushe.
Ta ce, “bayan na farfado ne na rika jin zafi a farji na, sai na fada wa mahaifiyata wadda ta kai kara ofishin ’yan sanda, inda suka bada shawarar a kai ni asibiti domin a duba lafiya ta.
“Likitocin sun tabbatar da an yi min kwakule a farjina, kuma da kananan raunuka a jikina,” inji ta.
Iyayen yarinyar Mista da Misis Timothy Bonko sun roki rundunar ’yan sanda ta tabbatar an hukunta masu laifin domin ya zama izina ga wadanda ke da niyyar aikata irin laifin.
Mahaifin yarinyar ya ce sun kai koke ga kungiyar Lauyoyin mata domin su bi wa diyarsa hakki.
Kwamishinan ’yan sandan jihar, Joseph Mukan ya ce a yanzu haka ana kan binciken lamarin.
“Gaskiya ne, mun san da faruwar lamarin, amma har yanzu bai zo teburina. Na san har yanzu ana kan gudanar da binciken ne,” inji shi.