✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama katan 185 na maganin karfin maza a Kano da Jigawa

Hukumar ta ce magungunan na da babbar illa ga al’umma.

Hukumar Hana Fasa-kwauri ta Kasa (NCS) ta ce ta kama wani nau’in maganin karfin maza da ake kira da AK-47 da sauran kwayoyi da darajarsu ta kai kusan Naira miliyan 200 a Jihohin Kano da Jigawa.

Kwanturolan hukumar, Suleiman Umar Pai ne ya bayyana hakan yayin da yake mika kwayoyin ga jami’in Hukumar Tabbatar da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), Shaba Mohammed a hedkwatar hukumar da ke Kano ranar Alhamis.

A cewar Kwanturolan, yawan kayan ya kai kimanin katan 185, yana mai cewa yawancin laifukan da ake aikatawa ana yin su ne bayan an yi mankas da miyagun kwayoyi.

Ya ce, “Yawan yadda ake ta’ammali da kwayoyin da ba su da rijista ko kuma suka lalace na da babbar illa ga mutane, musamman matasa.

“Yawancin ayyukan laifi ana yin su ne bayan ta’ammali da kwayoyi, saboda haka za mu ci gaba da yaki da su har sai mun ga bayansu,” inji Kwanturola Pai.

Sai dai ya sha alwashin cewa hukumar ba za ta yi kasa a gwiwa ba a yakin da take yi da fasa-kwaurin magungunan, tare da kira ga jama’a da su ci gaba da ba da hadin kai.

Shi ma da yake jawabi lokacin da yake karbar kayan, jami’in hukumar ta NAFDAC, Shaba Mohammed ya ce magungunan za su yi babbar barazana ga al’umma da ba a sami nasarar kwace su ba.

Mohammed ya bayyana kwace kayan da hukumar yaki da fasa-kwaurin a matsayin wani hobbasan hukumomin tsaro na aiki da juna kafada da kafada.

%d bloggers like this: