An kama tsoho Mataimakin Shugaban Majalisar Dattijan Najeriya, Ike Ikweramadu tare da matarsa a birnin Landan.
A cewar ’yan sandan birnin na Landan, an kama su ne kuma za a gurfanar da su a gaban kotu saboda shigo da yaro kasar ba bisa ka’ida ba.
- Miyagu na shirin jefa Najeriya cikin damuwa – Buhari
- INEC ta amince da kara wa’adin sabunta rajistar zabe
Sashen Kula da Laifuffuka na ’yan sandan birnin ne suka cafke shi tare da matar tasa, Beatrice.
A cewar kafar yada labarai ta Sky News, ana zargin mutanen ne da hada baki don cire wani sashe na jikin wani yaro, amma daga bisani an ceto shi kuma yanzu yana hannun kulawar gwamnati.
Kafar ta rawaito cewa, “Beatrice Nwanneka Ekweramadu mai shekara 55 da Ike Ekweramadu mai shakara 60, yanzu haka an tsare su a kurkuku, kuma za su bayyana a gaban kotun majistare ta Uxbridge a yau [Alhamis].
“An tuuhumi mutum biyun ne, wadanda dukkansu ’yan Najeriya ne, bayan wani bincike da sashen binciken laifuka na ’yan sandan birnin Landan suka gudanar.
“Yanzu dai an ceto yaron.
“An fara binciken ne bayan an ankarar da ’yan sanda kan laifin a ranar 22 ga watan mayun 2022, wanda wani salon bautar da mutane ne na zamani,” inji ’yan sanda.