✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘An kama hanyar warware rikicin kungiyar ’yan kasuwan Sakkwato’

Alhaji Kabiru Muhammad Tafida Sarkin Fada Sakkwato shi ne shugaban kungiyar ’yan kasuwa da masu masana’antu reshen Jihar Sakkwato. A wannan zantawar da Aminiya, ya…

Alhaji Kabiru Muhammad Tafida Sarkin Fada Sakkwato shi ne shugaban kungiyar ’yan kasuwa da masu masana’antu reshen Jihar Sakkwato. A wannan zantawar da Aminiya, ya yi karin haske game da ayyukkan cibiyar da nasarorin da ta samu da kudirinsu don habaka kasuwancin jihar da rikicin shugabancin kungiyar ‘yan kasuwa da sauran batutuwa.
Aminiya: Wadanne  ayyukka cibiyar kasuwanci da masana’antu ta Jihar Sakkwato take gudanarwa?
Alhaji Kabiru:Da farko dai cibiyar tana da rassa guda hudu gefen masana’antu da aikin gona da hakar ma’adanai da kasuwanci, ita cibiya ta kasance wata lema ce ta dukkan wadannan sana’o’i ita ce uwarsu da ke kulawa da sha’anin shiga da ficensu. Duk wani korafi ko neman bukata tsakaninsu da gwamnati a nan ne ake shirya ko gyara shi a takaice dai wannan cibiyar ita ce tsakanin gwamnati da su duk wani hakki ko taimako takan bai wa cibiya don a raba masu yadda yakamata. Ka ji kadan daga cikin ayyukan cibiyar.
Cibiya ta habaka kasuwanci a jihar nan a tun lokacin da na karbi jagorancinta a shekarar 2011 zuwa yau don na samu shugabanin da suka gabace ni sun yi iyakar kokarinsu kan haka na kudirci na daura saman nasu, sai na shiga wayar da kan ‘yan kasuwa su fadada kasuwancinsu zuwa wajen jihar da kasa baki daya, Misali kamar rika tafiya China kan haka muka yi kokarin kafa misali, inda muka tura mutane da kanmu har karo hudu kuma an samu nasara don dukkansu a yanzu suna huldar kasuwanci da kasar in da wasun ma ke kokarin kafa kananan masana’antu a jihar,  kafin haka sai dai su tsaya kasar Dubai kawai, abin da na fara sanya wa a gaba ke nan. Har ila yau, Allah Ya taimake ni na samu nasara, bayan wannan sai harkokin kasuwanci na cikin gida inda muke kokarin hada kan ’yan kasuwarmu wuri guda. Huldarmu da kananan ’yan kasuwa ta yi nisa sosai har ana shirin tallafa masu kuma suna shirin kafa kamfani na hadin gwiwa tsakaninsu mun yi ta taron karawa juna sani kan kasuwanci inda muke gayyato mutane ako’ina daga Kano da Legas da sauransu don sanin dabarun kasuwanci.
Aminiya: A makon da ya gabata ne jakadan kasar Pakistan ya ziyarci Jihar Sakkwato inda kuka kewaya da shi wuraren kasuwanci daban-daban wadanne irin nasarori ne ziyarar za ta samar?
Alhaji Kabiru:Wannan ziyarar an samu nasarori  kwarai da gaske, saboda shi Umar Faruk tsohon Janar ne na soja ya zo nan mun tattauna da shi kan hanyoyin hulda da kasar Pakistan don habaka kasuwancin jihar nan da kasarsa. Domin sha’awar hada hannu da jihohi irin namu masu albarkar kasuwanci da suke yi don haka za mu tafi can mu gane wa kanmu abubuwan da muke bukatar shigowa da su don amfanin jihar nan kamar kayan saka na maza da na mata irin su shadda da atamfa da leshi da kayan gini na zamani da sauransu duk suna da masana’antun da ke kerasu, lalle nan ba da jimawa ba zamu je Pakistan don gwamnatinmu na da sha’awa ga wannnan. Har ila yau, zaman da muka yi da shi ya yi mana amfani kwarai da gaske don ya kara wayarda kan ‘yan kasuwanmu kwarai da gaske.
Aminiya: kungiyar ’yan kasuwa tana cikin rikicin shugabanci, ta wace hanya za ku kawo karshen rikicin? Alhaji Kabiru: kungiyar ’yan kasuwa ta Arewa reshen Jihar Sakkwato haka sunan kungiyar yake  to saboda takaddama da aka samu kan rikicin shugabanci a karkashin Kabiru Hali to mun kira su a lokaci nan muka kafa kwamiti na sasantawa bayan nan gwamnatin jiha ma ta yi nata dukkanmu mun ba da shawara iri guda kan hanyar da za a kawo maslaha, cewa tun da kungiyar ta dade tana aiki ana iya yi mata garanbawul ko da babu abin da ya taso balle ga rigima, haka dai cibiya ta zauna da shugabanninta ta yanke shawarar rushe kungiyar gaba daya hakan aka yi. Yanzu kungiyar ba ta da shugaba ko na rikon kwarya ne babu kungiyar gaba daya yanzu, a halin da ake ciki cibiya ta kafa kwamiti na mutum 12 karkashin jagorancin Magajin Rafi Alhaji Mu’azu Bello a matsayin shugaba sakatare kuwa babban darakta na cibiya wannan kwamitin shi ne zai zama uba ga kungiyoyin ’yan kasuwa na jihar Sakkwato. Tun da wanda muka rushe yana jaggorantar kananan kungiyoyin ’yan kasuwa ne na jiha.  Mambobin an zabe su ne don cancantarsu baya ga cewa suma manyan ’yan kasuwa ne. Don haka ka sani su ne alhakin kula da ’yan kasuwa ya shafa har zuwa gaba cibiya ta san abin da za ta yi, na fito da wata sabuwar kungiya da za ta rika mu’amala da kananan kungiyoyin ’yan kasuwa da ba za su iya hulda da cibiyar ba.