✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama direba da ke tsafi da sassan jikin kananan yara

Ana zargin sa da safarar kananan yara yana tsafi da sassan jikinsu.

Rundunar ’Yan sanda a Uganda ta sanar da kama wani da ake zargi da safarar kananan yara yana tsafi da sassan jikinsu.

Mai magana da yawun rundunar ’yan sandan kasar, Fred Enanga wanda ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce za a mika mutumin Hedikwatar ’Yan sanda da ke Kampala, babban birnin kasar.

Mutumin da ake zargi wanda direban babbar mota ne, ya shiga ne hannu a garin Elegu da ke iyakar Arewacin Uganda a karshen makon nan.

Tun a shekarar 2011 ne manema labarai na BBC suka yi badda kama wajen nadar mutumin a wani hoton bidiyo kan yadda za a iya samun yaran sata.

Mista Enanga ya ce, sun san da ayyukan mutumin ne bayan da wani hoton bidiyo da aka nada shekara 10 da ta gabata ya bayyana a shafukan sada zumunta, inda aka nuna mutumin yana cewa shi shugaban wata kungiya ta masu satar yara su mika su ga ’yan kungiyar asiri.

Kakakin ’yan sandan ya yi kira ga duk wani wanda yake da bayani ya taimaka a yayin da suke ci gaba da gudanar da bincike a kan lamarin.