✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama daya daga cikin tserarrun fursunonin kurkukun Kuje a Ogun

Tuni ’yan sanda suka tisa keyarsa zuwa inda ya fito

’Yan sanda a Jihar Ogun sun sun cafke wani da ake zargin yana daga cikin fursunonin da suka tsere a harin da aka kai gidan yarin Kuje kwanan nan.

’Yan sandan sun ce, sun cafke Yakubu Abdulmumuni ne a yankin Sango-Ota da ke jihar.

Sanarwar manema labarai da Kakakin ’yan sandan jihar, DSP Abimbola Oyeyemi ya fitar a ranar Laraba, ta ce an kama wanda ake zargin ne a ranar Litinin da ta gabata.

Oyeyemi ya ce, sun samu nasarar cafke matashin ne biyo bayan bayanan da ofishin ’yan sandan yankin ya samu daga babban ofishin ’yan sandan jihar.

Ya ce, “Samun wannan bayanin ke da wuya, sai DPO na Sango-Ota, SP Saleh Dahiru, ya gaggauta hada kan jami’ai sannan aka tura su yankin inda a nan take aka damke mai laifin.

“Mai laifin shi da kansa ya tabbatar wa ’yan sanda lallai daga gidan gyaran hali na Kuje ya gudu a ranar 5 ga Yuli a lokacin da mahara suka kai wa gidan hari.

“Abdulmumuni ya kara da cewa, Babbar Kotun Jihar Kogi ta tura shi gidan yarin Kuje bayan da ta same shi da laifin hada baki da kuma kisan kai,” inji Oyeyemi.

Daga nan Kakakin ya ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, Lanre Bankole, ya ba da umarnin a dauki mai laifin zuwa inda ya fito ba tare da bata lokaci ba.

(NAN)