✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan tsohuwar Shugabar Laberiya da almudahana

A ranar Litinin da ta gabata ce jami’an tsaro a kasar Laberiya suka kama tare da gurfanar da dan tsohuwar Shugabar Kasar Misis Ellen Johnson Sirleaf…

A ranar Litinin da ta gabata ce jami’an tsaro a kasar Laberiya suka kama tare da gurfanar da dan tsohuwar Shugabar Kasar Misis Ellen Johnson Sirleaf a gaban kotu bisa laifin yi wa tattalin arzikin kasar makarkashiya, inda aka same shi da aikata almundahanar buga kudin kasar da suka kai miliyoyin Dalar Amurka ba bisa ka’ida ba.

Wanda ake tuhumar, mai suna Charles Sirleaf, ana zarginsa ne da mallakar wasu kudi da ya buga, a tsakanin shekarar 2016 zuwa 2018,  lokacin yana rike da mukamin Mataimakin Gwamnan Babban Bankin Laberiya.

Hudu daga cikin tsofaffin jami’an bankin su ma an kama su, yayin da biyu daga cikinsu suka tsere, ana nemansu. Zuwa yanzu dai dukan wadanda ake tuhumar ba su ce komai ba dangane da laifin da ake zarginsu da aikatawa.

A makon jiya ne dai aka fitar da wani sakamakon bincike na musamman da aka gudanar dangane da al’amarin.

Tsohuwar Shugabar Laberiya dai ta yi mukli ne a shekarar 2006 zuwa 2018, inda aka yaba mata cewa ta gudanar da mulki mai kyau, musamman yadda ta samar da tattalin arziki mai dama-dama a kasar.