✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan kwallo da bindiga a Binuwai

Matashin mai shekara 25 ya shiga hannu.

‘Yan kungiyar sa-kai a Jihar Binuwai (BSCVG) sun kama wani matashin dan wasan kwallon kafa mai suna Jeremiah Gbogo dauke da wata karamar bindiga a unguwar Fiidi da ke Karamar Hukumar Makurdi.

An kama matashin mai shekaru 25 sa’o’i 24 bayan mai bai wa Gwamna Hyacinth Alia na musamman kan harkokin tsaro da harkokin cikin gida, Cif Joseph Har, ya jagoranci wani gangami a Makurdi kan yaki da ayyukan da suka shafi kungiyar asiri, tashin hankali da barayi masu fasa shaguna.

Gbogo, wanda dan wasan kwallon kafa ne kuma manomi, ya zare bindigar da ake zargin ya karbo daga hannun abokin dan uwansa, tare da harba ta a iska, lamarin da ya kai ga shigarsa hannu.

Kwamandan ‘yan sa-kai na Jihar Binuwai, Kyaftin Ayuma Ajobi (mai ritaya), ya tabbatar da kama wanda ake zargin.