✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan fashin da ke farfesu da naman mutane

Jami’an ’yan sanda a Jihar Ribas sun yi katarin kama wani gawurtaccen dan fashi, mai suna Rowland Peter, wanda ke yin farfesu da naman naman…

Jami’an ’yan sanda a Jihar Ribas sun yi katarin kama wani gawurtaccen dan fashi, mai suna Rowland Peter, wanda ke yin farfesu da naman naman mutane yana ci.

Jami’an sun samu nasarar ce, bayan wani samame da suka kai wa maboyar wasu ’yan fashi da makami, wadanda kuma suke kama mutane suna garkuwa da su domin neman kudin fansa.

dan fashi Peter, halayyarsa ita ce idan ya kashe mutum yakan datse masa kai, ya cire masa hanta da kayan ciki, wadanda yake yin farfesu da su yana ci, kamar yadda ya bayyana wa ’yan sandan da suka kama shi. Har wayau sun ce suna zargin yana daya daga cikin wadanda suka kama wani fasto mai suna Samuel Okpara, suka yi garkuwa da shi, daga bisani kuma suka kashe a yankin karamar Hukumar Ahoada ta Gabas a kwanakin baya.

Da yake yi wa manema labarai karin bayani a ofishinsa yayin da aka gabatar da Rowland Peter da wasu mutum 22 da aka kama, Kwamishinan ’yan sanda a Jihar Ribas, Zaki Ahmed, ya ce mutanen yankin ba su iya runtsawa kafin a kama wadannan ’yan fashi. Sauran ’yan fashin da kwamishinan ya ce an kama sun hada Justus, wanda aka fi sani da lakanin High Tension.