✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama dan daudun da yake zagin kabarin mahaifiyar abokin fadansa na TikTok

A safiyar ranar Lahadi wani bidiyon TikTok da ya karade kafafen sada zumunta inda aka ga wani matashi ya raba kafa kan kabarin mahaifiyar wata…

A safiyar ranar Lahadi wani bidiyon TikTok da ya karade kafafen sada zumunta inda aka ga wani matashi ya raba kafa kan kabarin mahaifiyar wata da suka samu sabani a jihar Kano, yana yi mata zagin kare-dangi.

Bincike dai ya tabbatar da matashin dan daudu ne mai suna Abdullahi ‘Yar Dubu, mazaunin unguwar Sharada ne da ke jihar Kano.

Bayanai sun nuna hatsaniyar Tiktok ce ta hada shi da wani dan uwansa dan daudun, inda wancan ya zage shi, sai shi kuma ya mayar da martani da wannan salon.

Aminiya ta gano dai kabarin mahaifiyar abokin fadan nasa da aka ga ‘Yar Dubun na zagi na makarbartar Dan-Dolo ne a jihar Kano.

Wata majiya mai tushe ta bayyana mana cewa tuni ofishin ‘yan sanda na unguwar Sharada ta kamo matashin, ta kuma mika shi ga hedkwatar ‘yan sandan jihar da ke Bompai.

Mun yi kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar, SP Abdullahi Haruna Kiyawa kan lamarin, amma abin ya ci tura, kasancewar wayarsa na kashe.