✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama daliban Najeriya kan juyin mulkin kasar Turkiyya

Turkiyya za ta tisa keyar daliban Najeriya kan fataucin miyagun kwayoyi.

Gwamnatin Turkiyya ta kama daliban Najeriya biyu da ke karatu a Jami’ar Bahçeşehir da ke kasar a kan laifin zama mambobin kungiyar ta’addanci ta FETO/PDY.

Jakadan Turkiyya a Najeriya, Hakan Cakil, ya ce kasarsa za ta kuma koro wasu daliban Najeriya hudu kan laifin safarar miyagun kwayoyi.

Hakan Cakil ya ce daliban Najeriyan na daga cikin mutum 50 da ka kama kan alakarsu da Fethullah Gulen, dan Turkiyya mazaunin Amurka, wanda gwamnatin Turkiyya take zargi da yunkurin juyin mulkin da aka dakile a watun Yuli a kasar.

Ya ce a halin yanzu daliban da za a koro suna tsare a sansanin wadanda za a tisa keyarsu zuwa kashensu da ke Istanbul, babban birnin kasar ta Turkiyya.