Rahotanni na cewa dakataccen Kwamishinan Zaben Jihar Adamawa, Barista Hudu Yunusa-Ari ya fada komar jami’an ’yan sanda.
Muyiwa Adejobi, jami’in hulda da jama’a na rundunar ’yan sandan ne ya tabbatar da kama Yunusa-Ari a ranar Talata.
- Bafalasdinen da ya shiga yajin cin abinci ya mutu a gidan kaso a Isra’ila
- An yi gakuwa da ’yar Sauraniyar Kudancin Kaduna
Ya bayyana cewa ana ci gaba da gudanar da bincike a kan sauran wadanda ake zargi da haddasa rudanin da ya janyo cece-kucen da aka yi wajen ayyana sakamakon zaben Jihar Adamawa.
Yayin wata tattaunawa da BBC a ranar Litinin, Hudu Ari ya ce zai kai kansa ga ’yan sanda domin amsa tuhumar da ake yi masa.
Ya dai ce bai yi nadamar abin da ya aikata ba, don kuwa a cewarsa abin da ya yi yana kan doka.
Hudu Ari ya musanta zargin da ake yi cewa ya karbi cin hancin naira biliyan biyu, kafin ayyana Sanata Aishatu Binani a matsayin wadda ta yi nasara.
Tun bayan ayyana haramtaccen sakamakon zaben ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta ce Yunus Ari, ya yi layar zana.
Kwamishinan INEC na Kasa kan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama’a, Barista Festus Okoye, ya ce tun bayan da Barista Hudu Yunus Ari ya sanar da haramtaccen sakamakon zaben, ya daina amsa waya.
Tun a wancan lokaci Okoye ya bayyana cewa INEC ba ta san inda Barista Hudu ya shige ba, kuma bai kai kansa domin amsa tambayoyi a hedikwatar hukumar kamar yadda ta umarce shi ba.