Dakarun sojin Najeriya sun kama masu dillalan shanun sata 13 tare da kwato dabbobi 5,614 a hannunsu a Jihar Katsina.
Rundunar Tsaro ta Najeriya ta ce dabbobin sun hada da shanu 3,984, tumaki 1,627 da rakuma uku da aka kwato a cikin wata daya a fadin Jihar Katsina.
Mukaddashin Kakakin Rundunar, Birgideya Benard Onyeuko, ya ce dakarun Rundunar Operation Sahel Sanity, sun yi gagarumar nasara wurin dakilye ayyukan garkuwa da mutane da satar shanu da hare-haren ’yan bindiga daga cikin sauran manyan laifuka.
Oyeuko, a jawabinsa a Babban Sansanin Soji da ke Faskari, Jihar Katsina, ya ce rundunar ta taka muhimmiyar rawa wajen habakar yanayin tattalin arzikin al’amura a yankin Arewa maso Yamma.
An kafa Operation Sahel Sanity ne don agaza wa Operations Hadarin Daji wurin yakar ’yan bindiga, barayin shanu da masu garkuwa da mutane da sauran manyan laifuka a Arewa maso Yamma.
“Miyagun ayyukan sun yi sauki a yankin kuma ayyukan noma da sauran abubuwa na tattalin arziki na kara bunkasa.
“Sojoji sun kuma dakile hare-haren ’yan bindiga 74 da na garkuwa da mutane guda 54 a cikin wata daya”, inji shi.