An cafke wani matashi da ya tsallaka katanga ya sace wayoyi hannu guda 273 a wani gida.
Matashin ya fasa motar da mai gidan ya bar wayoyin da kudinsu ya kai Naira miliyan 15 ne a ciki, ya arce da su a garin Daura na Jihar Katsina.
- Azumin Bana: ’Da kyar muke samun abinci’
- Hattara dai mata: Mu yi wa kanmu fada kafin ranar da-na-sani
“Dubunsa ta cika ne bayan ya kutsa gidan a unguwar Shagari Low Cost a garin Daura, ya fasa motar mai gidan, ya debe wayoyin hannu 273 da kudinsu ya kai Naira miliyan 15,” inji kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, Gambo Isah.
Ya ce a yayin bincike ’yan sanda sun gano “Duk wayoyin guda 273 da ya boye a wurinsa, kuma ya amsa cewa aikata laifin.”
Da yake gabatar da wanda ake zargin, ya ce matashin tsohon fursuna ne kuma ya yi kaurin suna wajen fasa gidaje yana sace-sace.
“Da misalin karfe 7 na safiyar 22/04/2021 muka cafke matashin mai shekara 23 dan Unguwar Fegi da ke Daura, wanda sanannen barawo ne kuma tsohon fursuna, da ke fasa gidaje yana sace babura.”
Hafsan dan sandan ya ce za a gurfanar da wanda ake zargin a gaban kuliya, da zarar an kammala bincike.