✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kama barawon babur da ya kashe mutum a garin Aramako

Wani barawon babur da ake zargin shi ne ya kashe wani matashi mai sana’ar tukin babur ya shiga komar jami’an ’yan sanda a garin Aramako,…

Wani barawon babur da ake zargin shi ne ya kashe wani matashi mai sana’ar tukin babur ya shiga komar jami’an ’yan sanda a garin Aramako, Jihar Oyo.
dan uwan mai tukin babur din da barawon ya kashe, mai suna Sani Anas ya shaida wa Aminiya cewa kimanin makwonni biyu ke nan bayan sun idar da Sallar Isha’i sai ya ga marigayin mai suna Yahaya Isma’il ya dauki wani mutum a babur, suna cinikin kudin da zai ba shi. “Nan take na fada masa ina za ka kai shi cikin wannnan dare? Sai ya ce Ado Ekiti, sai na ce kada ya dauke shi domin dare ya yi saboda tafiyar kimanin awa daya ce. Ya ce mini ai yana so ya hada wani kudi ne, ya ce na yi wa mutumin magana ya ba shi Naira 1500 don shi ba ya fahimtar Turanci ko Yarabanci. Nan fa na yi masa magana sai ya dage kan Naira 1000. Marigayin ya nuna to ya kara masa 200 a kai wanda zai bai wa ’yan sanda sai yace ai ba a bukata don shi soja ne. Nan na bukaci ya nuna min katin shedarsa sai ya ce ai ya nuna wa marigayin. Da na tambaye shi sai ya ce eh haka ne, ya ga katin shedar. A haka ya dauke shi suka tafi, ashe barawon ba soja ba ne, shedar lasisin tuki ya nuna wa mamacin, ya yaudare shi domin shi ya dauka soja ne.” Inji shi.
Mutumin da ya ba marigayin hayar babur din, mai suna Bashir dansakkwato ya shaida wa Aminiya cewa tun lokacin da marigayin ya dauki barawon babur din, ba su sake jin duriyarsa ba sai da wani wanda shi ma a hannunsa ya sayi babur din ya kira shi ta waya, ya shaida masa cewa ’yan sanda ne suka tuntube shi sun kama wani da babur dinsa a Ibadan. “Nan take na sanar da shi cewa ai kimanin kwana 3 ake neman matukin babur din, sai nan take ya sanar da ’yan sandan domin su ci gaba da tsare shi.”
A nasu bangaren ’yan sandan sun shaida cewa sun kame barawon ne mai suna Olushola da dare misalin karfe, inda suka nemi ya ba su takardun mashin sai ya miko musu naira 200 sai suka ki karba. Nan fa sai ya rubanya kudin zuwa Naira 2000. Da suka ga haka sai suka gane ba shi da gaskiya, suka kame shi suka tafi da shi ofishinsu.
Malam Bashir dansakkwato ya kara da cewa da ’yan sanda suka matsa wa Olushola sai ya ce ai suna tafiya barayi suka tare su suka kashe mai babur din, shi kuma ya hawo babur din ya taho. Daga bisani ne bincike ya tsananta, ya fadi gaskiya cewa shi ne ya kashe shi ya kuma yadda ya nuna inda gawar take. Sai bayan da aka kwana takwas da kisan Yahaya, barawon ya nuna inda gawarsa take. “Abin da ya tayar mana da hankali domin mun tarar da gawar duk ta zagwanye, abin da ya sa ni zubar da hawaye. Nan fa muka bukaci a ba mu gawarsa, muka yi mata sutura.” Inji shi.
Mahaifin marigayin, Malam Sama’ila Garba ya shaida wa Aminiya cewa a lokacin da lamarin ya faru ya je gida Zamfara. Koda labarin ya riske shi na batan dansa sai ya dawo garin na Aramako. Ya ce marigayin dan kimanin shekara 27 ne kuma ya bar ’ya’ya biyu da mata biyu kuma a cikinsu akwai mai juna biyu don haka ya yi kira ga gwamnati da a tabbatar an hukunta wanda ya kashe masa dansa a kuma kwatar wa iyalan da ya bari hakkinsu.
Shugaban kungiyar ’yan Arewa mazauna garin na Aramako, Alhaji Garba Ibrahim Yariman Aramako ya ce ba su dauki doka a hannunsu ba don gudun cabewar lamarin, don haka ya yi kira da hukumar da lamarin ke hannunta da ta tabbatar an hukunta mai laifin. “Daman su barayin baburan sun dade suna kisan mummuke wa masu sana’ar tukin babur, koda muka fita neman gawar marigayin sai da muka ci karo da wata gawar, wacce ita ma a irin haka ne aka kashe mutumin. Maganar da nake yi har yanzu ba a dauke wannan gawar ba. Idan sun saci babur din sai su je da shi garin Ibadan, daman can ne dandalin hada-hadar baburan sata. In ban da rashin imani, ta ya za su dinga kashe rai a babur din da ba ya wuce Naira dubu 20 ko 30?” Inji Yariman Aramako.