✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kama barawo mai shigar Fatalwa a garin Gutu

Idan mutane sun tsere, sai ya tattara kayansu ya kama gabansa.

Rundunar ’Yan Sandan Zimbabwe ta kame wani barawo da ake zargi da fasa tagogin mutane a garin Gutu na gudunmuwar Masvingo da ke Kudancin kasar.

Kakakin rundunar ’yan sandan kasar, Paul Nyathi ne ya bayyana hakan wanda a cewarsa  ana ci gaba da gudanar da bincike domin tabbatar da zargin da ake yi wa mutumin.

Nyathi ya ce mutumin da ake zargi yana shiga irin ta fatalwa domin razanar wadanda ya je yi wa dan hali.

Sashen Hausa na BBC ya ruwaito cewa, ana zargin mutumin da yi wa wasu mutum biyu fashi da makami.

Nyathi ya ce, “Mutumin da ake zargi yana amfani da siffar fatalwa yana tsorata mutane, inda bayan mutane sun tsere, sai ya tattara kayansu ya kama gabansa.

“Har yanzu wanda ake zargin mai shekara 27 bai ce komai ba game da zargin da ake yi a kansa,” inji Nyathi.