✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An kai wa Sakataren Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta kasa hari

Ba na zargin kowa, kuma na dauki harin a matsayin kaddara, sannan Allah Ya kare ni.

Sakataren Tsare-Tsare na Hadaddiyar Kungiyar Kwadago ta Najeriya, Kwamared Nasir Kabir, ya tsallake rijiya da baya a wani hari da aka kai mai a hanyarsa ta zuwa rukunin gidajen ’yan majalisa da ke unguwar Apo a Abuja.

Kwamared Nasir ya sha da kyar ne a hanyarsa ta zuwa kai wa wani abokin huldarsa sako da misalin karfe 8 na dare ranar Lahadi.

Dan gwagwarmayar ya ce bayan harin, ’yan sanda da ke sintiri a yankin sun same shi domin tabbatar da abin da ke faruwa, sannan suka kai shi ofishinsu domin daukar bayanai.

Ya bayyana cewa daga bisani suka zarce da shi zuwa asibiti domin duba lafiyarsa saboda jijjigar da ya yi yayin kokarin kauce wa maharan.

Kwamared Nasir ya bayyana cewar ba ya zargin kowa, don ya dauki harin a matsayin kaddara, kuma Allah Ya kare shi.

Kwamared Nasir Kabir dai na daga cikin ‘yan gwagwarmayar da ke fafutukar tabbatar da an binciki Godwin Emefiele Gwamnan babban bankin Najeriya.

Aminiya ta yi kokarin jin ta bakin rundunar ‘yan sanda shiyyar Babban Birnin Tarayya, amma abin ya ci tura.